Tinubu ya nemi majalisar Dattawa ta tabbatar da Doro a matsayin minista

tinubu 2 (1)

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya rubuta wa majalisar dattawa wasiƙa yana neman tantancewa da tabbatar da Dr. Bernard Mohammed Doro daga jihar Filato a matsayin minista.

Majalisar ta karanta wasiƙar shugaban ƙasa a zauren ranar Laraba ta hannun shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.

Bayan karanta wasiƙar, Sanata Akpabio ya tura sunan wanda aka zaɓa zuwa kwamiti na majalisar domin yin nazari da bayar da rahoto cikin lokaci.

Nadin Doro ya biyo bayan naɗa Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC a watan Yuli, wanda a baya ya riƙe matsayin Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here