Jami’an tsaro da ke gadin fadar gwamnatin jihar Kano sun kama wani mutum da ake zargi da satar motar Toyota Hilux mallakar Gwamnati wadda guda ce cikin motocin da ke yiwa mataimakin gwamnan jihar rakiya.
Wati majiyar da ta tabbatar wa jaridar Solacebase a ranar Laraba cewa, wanda ake zargin, mai suna Ya’u Gezawa, yana daga cikin direbobin fadar gwamnati, kuma an kama shi ne a ranar Talata ta hannun jami’an tsaron fadar gwamnati, kuma yanzu haka yana tsare domin ci gaba da bincike kan lamarin.
A baya, jaridar Daily Nigeria ta bayar da rahoton cewa an sace motar Toyota Hilux da ke cikin rakiyar mataimakin gwamnan daga harabar fadar gwamnati da safiyar Litinin, inda aka ce an fitar da motar ta ƙofar fadar mai lamba 4 da misalin ƙarfe 5 na safe ba tare da jami’an tsaro sun dakatar da shi ba.
Bisa ga majiyar cikin gida, har yanzu gwamnatin jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba, sai dai an bayyana cewa an samu nasarar kama wanda ake zargin ne ta hanyar bayanan sirri da sashen tsaron fadar gwamnati ya fitar.
Karanta: Ɗan majalisar tarayya a Kano Sagir Koki ya fice daga jam’iyyar NNPP
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron fadar sun gudanar da bincike mai zurfi wanda ya kai ga gano inda wanda ake zargin yake kafin a cafke shi.













































