Omicron: Saudiya ta haramtawa ‘Yan Najeriya shiga kasar

WhatsApp Image 2021 12 08 at 5.22.10 PM
WhatsApp Image 2021 12 08 at 5.22.10 PM

Gwamnatin kasar Saudiya ta sanar da hana jiragen sama da suka tashi daga Najeriya shiga kasar sakamakon samun wasu ‘yan Nigeria dake dauke da sabon nau’in cutar korona da ake kira Omicron.

Hukumar dake kula da harkokin jiragen sama ta kasar Saudiya ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a yau laraba mai dauke da sa hannun mataimakin shugaban hukumar mai lura da bangaren tattalin arziki da zirga-zirgar jiragen sama.

Sanarwar tace an bada umarnin dakatar da sauka da tashin jiragen da suke zuwa kai tsaye daga Nigeria, sai dai idan mutanen da suke ciki sun yi a kalla kwanaki 14 a wata kasa daban.

Sanarwa tace ‘yan kasar wanda suka dawo daga Nigeria zasu killace kansu a gida na kwanaki biyar, inda ta bayyana cewa duk wanda ya karya wannan doka zai fuskanci hukunci mai tsauri.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here