Jiragen sama biyu sun yi karo a Kenya

Jiragen saman, Kenya, karo
Hukumar da ke sanya ido kan sufurin jiragen sama a ƙasar Kenya ta tabbatar da cewa jirgin Fasinja na Safarilink ya yi karo da wani jirgin da ke atisaye a...

Hukumar da ke sanya ido kan sufurin jiragen sama a ƙasar Kenya ta tabbatar da cewa jirgin Fasinja na Safarilink ya yi karo da wani jirgin da ke atisaye a sama.

An fara bincike don gano abin da ya haddasa hatsarin.

“An fara bincike mai zurfi ta bangarorin hukumomi da dama, wanda ma’aikatar binciken hatsarin jiragen sama za ta jagoranta da kuma hukumar ‘ƴan sanda ta ƙasa don gano musabbabin hatsarin” a cewar hukumarsa ido a kan sufurin jiragen sama na ƙasar.

Karin labari: Amurka ta ƙaƙabawa shugaban Zimbabwe sabbin takunkumai

Mutane biyu da ke cikin jirgin da ke atisayen duk sun mutu, amma an samu ceto fasinjoji 39 da ma’aikatan jirgin Safarilink biyar.

Kamfanin jiragen Safarilink ya bayyana a shafinsa na X cewa, jim kaɗan bayan tashin jirgin ne da misalin ƙarfe 3. 45 agogon ƙasar, aka yi wata ƙara mai ƙarfi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here