Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da nadin Farfesa Amina Salihi Bayero a matsayin shugabar jami’ar Northwest ta Kano na tsawon shekaru biyar da naɗin ya fara aiki daga Litinin, 1 ga Disamba 2025.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis ta bayyana cewa nadin ya biyo bayan shawarar da kwamitin gudanarwar jami’ar ya bayar bayan wani tsari na tantancewa mai tsauri.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa tun bayan kafuwar jami’ar a shekarar 2012, Farfesa Amina Salihi Bayero ce mace ta farko da aka nada shugabar jami’a Mace.
Gwamna Yusuf a matsayinsa na mai sa ido kan jami’ar ya yaba wa shugaban kwamitin gudanarwar jami’ar da sauran mambobi bisa jajircewarsu wajen mutunta cancanta da gaskiya a tsarin tantancewar.
Karanta: Gwamnatin tarayya ta kafa cibiyoyin koyarwa 119 domin inganta ilimin Almajirai
Ya kuma roki addu’o’in samun jagorancin Allah ga sabuwar shugabar jami’ar yayin da za ta fara gudanar da nauyin aikin da ke gabanta.
Farfesa Amina Salihi Bayero kwararriya ce a ilimin “Analytical Chemistry” kuma ita ce mace ta farko da ta kammala digirin digirgir a fannin Chemistry daga jami’ar Bayero Kano.
Ta yi aiki a manyan mukamai na ilimi da gudanarwa ciki har da shugabar sashen ilimi, shugabar tsangayar kimiyya da mataimakiyar shugabar jami’a a jami’ar Yusuf Maitama Sule, inda ake girmama ta kan bincike, jagoranci da kuma jajircewa wajen ba matasa masana goyon baya.













































