Alfijr ta rawaito Dan takarar Mataimakin Gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APC, Alh. Murtala Sule Garo ya caccaki gwamnatin tarayya kan tsarin sanya wa’adi na daina karbar tsaffin kudade samfurin naira 200, 500 da 1000.
Murtala Garo ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a gangamin taron yakin neman zaben jam’iyyar APC a karamar hukumar Dambatta.
Garo ya yi gargadin cewa ba za su zauna su nade hannu anaiwa al’ummar Kano cin kashi, wadanda akasari ‘yan kasuwa ne shan wuya tare da barazanar gurguncewar kasuwancin su sakamakon mummunar manufar da babban bankin Najeriya ya fito da su.
Ya kuma tunatar da cewa Najeriya na tafiya akan tsarin mulkin dimokuradiyya, inda ake mutunta ra’ayoyin al’umma sabanin abin da yake faruwa a tsarin mulkin soji, amma duk da haka anki mutunta ra’ayoyin mutane.
“Yanzu fa mulkin siyasa muke yi ba mulkin soja ba, al’umma suna cikin razani da kunci, a barmu mu kashe kudin da muke dashi”. A cewar Murtala sule Garo
”Shi chanjin kudin ba shi ne matsalar al’umma a yanzu ba, matsalar ita ce a bar al’umma su kashe kudaden hannun su a hankali har sabbin su wadaci al’umma “.inji Murtala Sule Garo
Daga ya shawarci al’umma dasu gaggauta sauya kudaden nasu cikin bankuna, kada abarsu abaya.













































