Wani dagorin fadar gidan sarautan Birtaniya ya yanke jiki ya fadi a kan mimbari inda ya ke gadin akwatin gawar sarauniya Elizabeth ta II.
A cewar Mirror, yan sanda sun garzaya sun taimaka masa bayan ya fadi kasa.
Mutane da dama sun yi layi a titunan Landan domin ganin gawar sarauniyar da ke dakin taro na Westminster gabanin birne ta a ranar Litinin 19 ga watan Satumba. Sojoji sun yi fareti da akwatin gawar daga fadar Buckingham a ranar Laraba, 14 ga watan Satumba. Bisa, alamu daya daga cikin dogarin ya gaza jurewa hakan yasa ya fadi sumamme.
Mutane masu zaman makoki sun yi mamaki a lokacin da ya fadi kasa kamar yadda bidiyon ya nuna. Ya faru ne a lokacin da dogaran ke shirin sauya aiki amma daya cikinsu ya yanke jiki ya fadi.
An ga yan sanda biyu sun tafi su taimaka masa kafin bidiyon ya yanke sannan sai aka fara nuna hotunan majalisun Birtaniya.
Mutane da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu kan bidiyon inda wasu ke cewa juyayin rasuwar Sarauniyar ne ya kidima shi.










































