Dubban ‘yan Najeriya ka iya rasa zuwa aikin Hajjin 2025 yayin da NAHCON ta kawo karshen yarjejeniyarta da Saudiyya

NAHCON NEW NEW 750x300

Kungiyar manyan jami’an hukumar jin dadin Alhazai ta jihohi har ma da hukumomi sun koka kan cewa dubban maniyyatan Najeriya ba za su iya zuwa aikin Hajjin 2025 ba saboda kawo karshen yarjejeniyar da shugaban hukumar kula da Alhazai ta kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya yi da mahukuntan Saudiyya.

Sakataren kungiyar kuma babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Adamawa, Abubakar Salihu, wanda ya yi magana a madadin kungiyar, ya yi wannan tsokaci ne a wata hira da manema labarai a ranar Lahadi.

Taron ya kunshi manyan shuwagabannin hukumomin jin dadin Alhazai na jiha, Hukumomi, da kwamitocin Jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

Salihu ya ce, matakin da shugaban NAHCON ya dauka na rattaba hannu kan kawo karshen yarjejeniyar da kamfanin kula da alhazai Saudiyya Mashariq AL-Dhahabiah na iya hana ‘yan Najeriya bizar aikin Hajjin 2025, tare da hana su zuwa aikin Hajji mai tsarki.

“Ya zama dole kuma a sanar da jama’a cewa idan maniyyatan Najeriya masu niyyar zuwa aikin Hajji na 2025 ba su samu ba, su rike shugaban hukumar NAHCON, kada su zargi hukumar alhazai ta jiha. Ya kamata a zargi shugaban NAHCON,” in ji sakataren kungiyar.

Sakataren kungiyar ya bayyana cewa shugabancinsu ya gana da shugabannin hukumar NAHCON tsakanin ranakun 15 – zuwa 17 ga watan Janairu domin zabar Mashariq Al-Dhahabiah da zai yi wa alhazan jihar hidima a Muna, Arafat da Muzdalifah, inda aka zabi Rawaf Muna dai zai yi hidima ga mahajjata na musamman (VIP).

Kungiyar ta yi mamakin dalilin da ya sa NAHCON za ta baiwa masu gudanar da yawon bude ido, wadanda ba su kai kashi 20 cikin 100 na alhazan Nijeriya ba, su zabi mai musu hidimar da suke so, kuma sun hana jihohin, sama da kashi 80 cikin 100 na alhazai 95,000 su zabi ra’ayinsu”.

Kimanin ‘yan Najeriya dubu 50,000 ne ake sa ran za su yi aikin Hajjin bana a karkashin kason da jihar ke da shi, yayin da wani kashi daya cikin hudu na adadin ke karkashin kason masu yawon bude ido.

Rahotanni sun ce shugaban hukumar NAHCON na kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya ne domin nada wani ma’aikacin da bai taba yi wa alhazan Afirka hidima ba, ballantana na Najeriya – wanda hakan ka iya cutar da alhazan Najeriya.

Wani jami’in hukumar da ya yi magana a cikin kwarin gwiwa ya ce tuni aka aike da koke ga hukumomin bincike domin soke kwangilar.

Ya bukaci babban mai shari’a kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, SAN, da ya sa baki a cikin wannan lamari na kwangilar Masha’ir domin ceto Najeriya daga badakala.

Ko da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar Hajiya Fatima Sanda Usara, ba ta iya cewa komai ba saboda ba a yi mata bayani kan lamarin ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here