Shugaban Majalisar Jihar Ribas, Barista Ehie Edison ya ayyana kujerun ‘yan majalisa 27 da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a matsayin wadanda ake da gyibin su.
Shuagaban ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da ya jagoranci zaman majalisar dokokin jihar karo na 10.
Karanta wannan:JAMB zata fara Jarrabawar auna fahimta ga masu neman shiga Jamia’a kai tsaye
Idan za a iya tunawa ‘yan majalisar dokokin jihar 27 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar Litinin.
Haka kuma wata babbar kotu a jihar a ranar Talata ta bayyana Edison Ehie a matsayin sahihin shugaban majalisar dokokin jihar.
Kotun karkashin jagorancin mai shari’a M.W. Danagogo ta garagadi Martins Amaewhule kan ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban majalisar.