Shugaban kasa Bola Ahamed Tinubu ya amince da kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha a babban birrinin tarayya Abuja dake yankin Gwarinpa, wadda aka saka sunan sa.
Kwalejin, mai suna Bola Ahmed Tinubu Polytechnic, Gwarinpa, tana da burin inganta ilimin fasaha, sana’o’i, da kuma harkokin kasuwanci daidai da manufofin kasa na Najeriya kan ilimi.
A wata wasika mai dauke da kwanan watan 16 ga watan Janairu, 2025, kuma aka aika wa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya tabbatar da amincewar gwamnatin tarayya da. Wasikar mai dauke da sa hannun Alausa, ta bukaci Wike da ya ba da shawarar wuraren da suka dace da wuraren wucin gadi da na dindindin na kwalejin kimiyya da fasaha a Gwarinpa.
Ana sa ran wata tawagar fasaha daga ma’aikatar ilimi ta tarayya da hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE) za su ziyarci wuraren da aka tsara don duba kwalejin.
Ana sa ran sabuwar kwalejin kimiyya da fasaha za ta bunkasa damar samun ingantaccen ilimin fasaha da na sana’a a cikin babban birnin tarayya Abuja, tare da kara karfafa kokarin Najeriya na bunkasa fasaha da kirkire-kirkire.
Shugaban hukumar Abuja Municipal Area Council (AMAC), Christopher Zakka Maikalangu, ya yabawa shugaba Tinubu kan amincewa da sabuwar kwalejin, inda ya bayyana shi a matsayin wani gagarumin ci gaba ga babban birnin tarayya Abuja.
“Kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya a Gwarinpa abuda nake mafarki ne, kuma zata ba da gudummawa ga ci gaban mazauna FCT,” in ji Maikalangu.