2025: Hukumar Alhazai ta Kano Ta Fara Horar Da Alhazai

Danppa 694x430.jpeg

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta fara gudanar da aikin horar da Alhazai na 2025 a cibiyoyi tara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sulaiman Dederi ya sanyawa hannu kuma ya raba wa manema labarai a ranar Talata a Kano.

Dederi ya nakalto Darakta Janar na hukumar Alhaji Lamin Danbappa ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da Malamai (Malaman Musulunci), wadanda za su jagoranci kwas din karawa juna ilimi a cibiyoyi daban-daban a fadin jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here