Gwamnatin jihar Kano bankadu wata ma’ajiya da aka ajiye gurbataccen taki mai yawan gaske a Gunduwawa dake karamar hukumar Gabasawa.
Shugaban hukumar kare hakkin mai siya da mai siyarwa ta jihar Kano, Baffa Babba-Dan’agundi, ne ya bayyana hakan ta bakin mai magana da yawun hukumar, Musbahu Yakasai yau Laraba a Kano.
“Mun sami bayanan sirri cewa akwai wani mamallakin ma’ajiyar taki yana hada takin da yashi, sanan ya siyarwa manoma.”
“Hakan yasa muka dau matakin rufe ma’ajiyar, domin kare al-ummar jihar Kano daga amfani da taki mara kyau.” Inji shi.
Yakasai ya kuma kara da cewa a baya ma hukumar tasu ta kama wata mota a cike da semovita mara kyau a kasuwar Singa, sanan kuma hukumar ta kara kama wata ma’ajiyar takin mara kyau a karamar hukumar Garko.
Ya kuma nema al-umma da su cigaba da bawa hukumar bayanan irin wadan nan gurare domin kare rayukan al-umma.