ASUU ta yi watsi da yunkurin gwamnatin tarayya na karin kudin da dalibai ke biya a jami’o’in kasar nan baki daya

ASUU ASUU NEW
ASUU ASUU NEW

Kungiyar malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU ta yi watsi da yunkunrin gwamnatin tarayya na kara kudin makaranta a Jami’o’in kasar nan baki daya.

Shugaban kungiyar reshan jami’ar Jos, Dakta Lazarus Maigoro, ne ya bayya na hakan yau Laraba yayin zan-zangar da kungiyar NLC ke gudanarwa a fadin kasa baki daya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaitu cewa kungiyar NLC ta shiga zan-ga zan-gar domin marawa ASUU baya, don ganin ankawo karshen yajin aikin da ASUU kiye.

Maigoro ya zargi gwamnatin da yunkurin karin kudin makaranta ya kuma N750, 000 ga kowane dalibi, ya ce yajin aikin na daya daga kokarin kungiyar na dakatar da gwamnatin daga kara kudin makarantar.

Ya kara da cewa da zarar gwamnati ta kara kudin makarantun, ba makawa ‘ya ‘yan talakawa sun bar zuwa makaranata kenan.

Maigoro ya kuma bukaci gwamnatin tarayya data aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla da ita tun 2009, da kuma yarda tsarin biyan albashi na UTAS.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here