Gwamnan jihar Kwara AbdulRaham AbdulRazaq, ya ziyarce Balogun Alanamu na Ilorin, Dr Usman Abubakar Jos, domin jajantawa wadan da shagunan su suka kone, a hatsarin gobarar da ta tashi a kasuwar Alanamu.
AbdulRazaq ya ce gwamnatinsa zata bada tallafin rage radadi ga wadan da iftila-in ya rutsa dasu.
Gwamnan ya yiwa Balogun Alanamu ta’aziyar rasuwar matar sa Hajia Saadah Iyabo, da kuma Alhaji Sa’adudeen Alagola ranar Lahadi.
Ya kuma yabawa hukumar kashe gobara ta jihar, bisa bayar da agajin gaggwa da suka yi yayin da gobarar ta tashi.
Balogun Alanamu ya jagoranci gwamnan zuwa shaguna 15 da suka kone sakamakon gobarar, sanan kuma ya yabawa gwamnan bisa agajin gaggawa da ya bayar.
Sanan kuma ya bukaci gwamnan da rubanya akan kokarin da yake wajan samarwa da hukumar kashe gobara kayan aiki.
“ Muna godewa mai girma gwamna bisa agajin gaggawa da gwamnatin ka ta bayar, wanan kasuwa tanada shaguna 90, Allah ne ya takaita wutar da tsaya kadai a kan shaguna 15”
Balogun ya kuma yiwa gwamnan addu’ar gama mulkin sa lafiya”













































