Cibiyar horar da ma’aikatan hukumar Alhazai ta Ƙasa zata fara zangon karatu na farko

HIN nahcon 1
HIN nahcon 1

Cibiyar horar da ma’aikatan hukumar alhazai ta kasa ta Samar da Cibiyar bada horo wanda zasu fara shirin bada horon zangon karatu na farko na 2023/24, a ranar Talata 7 ga watan Fabarairun shekarar 2023, da dalibai a matakin farko.

Rahotanni sun ce shirin Wanda ake saran Ministan ilimi, Adamu Adamu ne zai rantsar da daliban karo na farko, yayin da ministan birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, zai zama babban bako na musamman a gurin bikin kadammar da zangon.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai na hukumar, Mousa Uban Dawaki, ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ce cibiyar zata fara da bawa ma’aikatan hukumar horo na makonni hudu tareda mika takardun shedar kammala daukar horon kan yadda ake gudanar da aikin hajji da umara cikin kwarewa.

Shugaban hukumar alhazai ta kasa Alh Zikrullah Kunle Hassan, ya bayyana farin cikin sa da fara aikin da cibiyar zatayi.

“Ina taya dukkan masu ruwa da tsaki na wannan hukumar bisa wanann gagarimin nasara da aka samu, wanan nasarar da aka samu nada alaka da namijin kokarin da tsaffin shuwagabanin hukumar suka yi, saboda haka ina jan hakanlin dukkan masu ruwa da tsaki na wanan hukumar da su hada karfi da karfe don ganin cigaban wannan cibiyar bada horo.”

Kafa cibiyar na daya daga cikin manufofin shawagabanin hukumar na yanzu, don ganin an sami kwararunrun jami’ai da zasu gudanar da aikace aikacen hukumar ya yin aikin hajjin bana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here