Muslim-Muslim: Kotu Ta Yi Fatali da Karar da Aka Shigar da Tinubu da Shettima

6297b614586fe7a0
6297b614586fe7a0

Babbar Kotun tarayya mai zama a birnin tarayya Abuja ta yi fatali da ƙarar da aka shigar da Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa a APC.

Alkalin Kotun mai shari’a Ahmed Ramat Mohammed shi ne ya yi fatali da karar, wacce aka bukaci soke takarar Tinubu kan haɗa tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2023.

Channels tv ta rahoto cewa wani Lauya a Abuja, Mista Osigwe Momoh, ne ya shigar da karar kuma Alkalin ya fatattaki bukatarsa ne saboda lauyan ba shi da ikon sa baki a batun.

Mai shari’a Mohammed ya bayyana cewa kasancewar lauyan ba mamba bane a APC kuma ba da shi aka bi matakan samar da Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima ba, ba shi da hurumun kalubalantar takararsu.

A ƙarar da ya shigar, lauyan ya roki Kotu ta haramtawa APC da Tinubu shiga zaben shugaban ƙasa mai zuwa bisa Hujjar haɗa takara Musulmi da Musulmi.

A cewar Lauyan matakin ya saba wa kundin tsarin Mulkin Najeriya kuma ya yi karan tsaye ga sashi na 14, 15 Da 224 a kwansutushin ɗin Najeriya 1999.

Haka zalika mai shigar da karar ya nemi Kotu ta dakatar da hukumar zabe INEC daga sanya sunan APC da ɗan takararta na shugaban kasa dangane da zaben 2023.

Sai dai a hukuncin da Kotu ta yanke, mai shari’a Mohammed, ya ƙi yarda da musun Lauyan game da damar da doka ta bayar na kai kara kan batun kana ya yi watsi da ita baki ɗaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here