Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta jajantawa gwamnatin jihar da karamar hukumar Lafiya bisa rasuwar mutane 12 a wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a kogin Kogi Kungra Kamfani da ke Arikiya a karamar hukumar Lafia.
Shugaban majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi ne ya bayyana haka yayin wani zaman gaggawa da majalisar ta gudanar a garin Lafiya babban birnin jihar a ranar Alhamis.
Ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka rasu bisa rasuwar ‘yan uwansu.
“Abin takaici ne yadda muka rasa mutane 12 da suka hada da maza da mata a wani hatsarin kwale-kwale a Arikiya da ke karamar hukumar Lafia.
“Mutane 19 ne ke cikin jirgin, 12 sun mutu sannan 7 sun samu ceto. An jefa karamar hukumar Lafiya da jiharmu cikin alhini kan wannan abin bakin ciki da ya faru,” inji shi.
Majalisar ta bukaci dangin, karamar hukumar Lafiya, da kuma gwamnatin jihar da su dauki wannan rashi matsayin kaddara.
“A madadina, ‘yan majalisa, da ma’aikata, muna jajantawa iyalan mamatan, karamar hukumar Lafiya, da gwamnatin jihar bisa wannan rashi. Muna addu’ar Allah ya jikan su,” Shugaban Majalisar ya kara da cewa.
Shugaban majalisar ya yi addu’ar Allah ya gafarta musu kurakurensu, ya kuma sa su huta.
‘Yan majalisar dai sun yi shiru na minti daya domin karrama su.
NAN