Babbar kotun jihar Filato da ke zamanta a Jos ta bayar da umarnin dawo da Abok Ayuba a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar Filato da aka tsige.
Kotun ta bayar da umarnin ne yayin zamanta ba yau Litinin.
Yan majalisar dokokin jihar sun tsige Abok Ayuba ne a ranar 28 ga Oktoba, bara, sai dai tun a lokacin ya kalubalanci tsigewar da ya bayyana ta a matsayin abida ya saba wa ka’idar majalisar.
Alkalin kotun, Mai shari’a Nefisa Musa, wadda ta yanke hukuncin, ta amince da roko da karar da ya shigar a kotu.
Alkalin ta ce, tsarin da aka bi na cire Ayuba ya saba wa doka.
Aboka Ayuba, ya godewa jama’ar jihar Filato da suka taya shi jaje da jimami daga lokacin tsige shin har zuwa samun nasararsa.
“Har yanzu muna da sauran watanni da za mu ci gaba da yin aiki a mazabunmu ga al’ummar da suka zabe mu.
“Duk da cewa an yi rikici a wasu lokutan baya, amma a yau kotu ta ba da wadannan sharuddan na dawo da ni kasancewar abinda aka yi ya saba wa doka,” in ji shi.
Haka kuma, ya ce da yardar Allah zai ci gaba da aiki cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.
Ayuba ya ce ba zai yi fada da kowa ba, ya kara da cewa dukkansu ‘yan majalisar ne kuma duk ‘yan Filato ne kuma ‘yan Najeriya.
A cewarsa, za su yi aiki tare domin ci gaban Filato da Najeriya.
“A shirye nake in yi aiki tare da bangaren zartaswa, ba mu taba cewa ta kowace hanya ba, zan so in ci gaba da aiki da su, Wannan ne kawai zai ba mu zaman lafiya a jihar nan”.
“Duk wanda ya kasance a kotu a yau ya san cewa kotu ta bayyana komai game da wannan tsigewar,” in ji shi.
NAN













































