Kungiyar WOFAN da masu ba da shawara daga cibiyar binciken hatsi da inganta shi ta kasa (NCRI) da ke Badegi a jihar Neja, sun fara ayyuka da nufin inganta abinci, samar da ayyukan yi masu inganci ga matasa, musamman mata da masu bukata ta musamman a Najeriya.
Shirin ya gindaya kyawawan manufofi a shekarar 2025, wadanda suka hada da rage noman shinkafa da asara bayan girbi, da kara hanyoyin samun kudin shiga ga kananan manoma da masu sarrafa kayayyaki, da inganta samar da abinci ta hanyar dabarun zamani.
WOFAN ta gudanar da kwarya-kwaryar taron a Abuja domin kaddamar da sabbin ayyukan sabuwar shekara, wanda ya samu halartar kungiyoyin mata daga jihohin Adamawa, Bauchi, Benue, Gombe, Kaduna, da Nasarawa, wadanda suka hada da malaman gona da kuma masana.
Taron ya mayar da hankali ne kan tsara sabbin hanyoyin, dabarun inganta tattalin arziki da darajar shinkafa, da nufin samar da kyawawan kayayyaki da matane zasu so siya.
A yayin taron Hajiya Maimuna Lawal, Daraktar samar da dabaru, kirkire-kirkire, da dorewar shirin WOFAN-ICON2, ta bayyana cewa kashi 30 zuwa 40 na shinkafar da ake nomawa a Najeriya ana asarar ta ne ko kuma a barnatar da ita ta hanyar da ta dace.
A cewarta, irin wadannan asara na faruwa ne sakamakon kwari da cututtuka, da yin ayyukan noma ba bisa tsari bada ba, rashin kula da su da amfanin gona, da kuma rashin samar da kayan aiki.
Don magance wadannan matsaloli, Hajiya Maimuna ta jaddada muhimmancin samar da sabbin dabaru wajan girbi da sarrafa amfanin gona, inda tace hakan zai taimaka wajan mayar da asarar da aka yi da kuma kara samun kudin shiga.
A nasa jawabin, Jami’in Cibiyar binciken Hatsi da inganta shi (National Cereals Research Institute Badegi) dake jihar Naija, Dakta Danbaba Nehemiah, ya ce hadin gwuiwar za ta taka muhimmiyar rawa wajen sarrafa amfanin Gona musamman Shinkafa ta fuskoki da dama.
Dokta Nehemiah Danbaba, kwararre kan noman shinkafa daga NCRI, ya jaddada yuwuwar kara darajar ta wajen sauya shinkafa mara inganci zuwa kayayyaki masu daraja. Ya buga misali da fasasshiyar shinkafa, wadda akasari ake ƙi bayan an raba ta, wadda za a iya niƙa ta ta zama gari don ƙirƙirar sabon samfuri tare da aikace-aikace iri-iri.
Irin waɗannan sabbin abubuwa, a cewarsa, na iya ba da gudummawa sosai ga ingantattun abinci mai gina jiki da kuma bunkasa tattalin arziki ga mata da sauran al’umma.
Hajiya Salamatu Garba, shugabar ayyukan WOFAN-ICON2 ta kasa, ta bayyana cewa shirin ya yi daidai da burin gidauniyar Mastercard na samar da ayyukan yi masu inganci ga matasa kimanin miliyan 10 da suka hada da mata da masu bukata ta musamman.
Ta kuma kaddamar da fara aikin shekarar 2025 ne ta hanyar yanka cake wanda aka yi shi da shinkafa da garin gyada tare da baje kolin wasu sabbin kayayyaki, irin su buhunan shinkafa da ake amfani da su wajen yin briquettes da taki.
Ta ce shirin na shekarar 2025 ya hada da bullo da injunan sarrafa shinkafa daban-daban da kuma gina kwazon matasa don yin sana’o’i masu inganci.
Sauran shirye-shiryen sun hada da ingantawa da karfafa shinkafa da muhimman abubuwan gina jiki da hada ta da sauran amfanin gona irin su waken soya da gyada domin samar da ingantacciyar shinkafa da fulawa.
Ta hanyar haɗin gwiwa tare da ƙungiyoyin bincike wadan da suka dace da gudanarwa da aiwatar da sabbin ayyuka, aikin yana da nufin ƙarfafa mata da matasa kan dabarun sarrafa shinkafa.
Mista Taiwo Olawale, Manajan Ayyuka da Kasuwanci na WOFAN, ya kammala taron da cewa: “Yin nasarar aiwatar da wadannan tsare-tsare na iya ba da dama ga ci gaban tattalin arziki, da inganta samar da abinci mai gina jiki, wanda zai haifar da riba mai yawa. ga al’ummar da abin ya shafa.”