Ƴan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjoji jirgin ƙasa sun sako wata mai juna biyu

Abducted pregnant woman
Abducted pregnant woman

Ƴan ta’addan da suka kai harin bam a kan jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna da suka kashe mutane tara tare da yin garkuwa da fasinjoji kusan 70 a watan Maris, sun sako wata mata mai ɗauke da juna biyu.

An dai nuno matar da aka saki ɗin a cikin wani faifan Bidiyo tana sanye da baƙar abaya da abun rufe fuska inda aka yi ta yaɗa hoton a kafafen sada zumunta.

Bincike ya nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun sako matar ne bisa tausayawa bayan ta shafe kwanaki 48 a hannun wasu.

Shafin jaridar The Nation ya ruwaito, a cikin faifan bidiyon, matar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tattauna da ƴan ta’addar tare da ganin an sako sauran wadanda suka yi garkuwa da su.

Ta ce, kiran nata ya zama wajibi saboda halin rashin tabbas da mutanen ke ciki a maɓoyar ƴan bindigar.

Haka kuma, Matar ta ce ƴan ta’addar sun kula da su, inda ta ƙara da cewa suna ba su abinci sosai.

Ta kuma ce ‘yan ta’addan suna ba su magunguna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here