Girgizar kasa ta hallaka sama da Mutane 100 a China

AP23353134072567
AP23353134072567

A kalla mutane 116 ne suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta ruguje gidaje a arewa maso yammacin kasar China.

Tuni dai tun a safiyar ranar Talata kafafen yada labarai na kasar suka rawaito jami’an ceto sun dukufa wajen tona baraguzan gine-gine cikin wani yanayi mai sanyin gaske.

Jami’ai a lardin Gansu da lamarin yafi muni sun ce kimanin mutane 105 ne suka mutu sannan kusan 400 suka jikkata.

Karanta wannan: Majalisar Dokokin Adamawa ta amince da kasafin shekarar 2024

Rahotanni sun tabbatar da cewa girgizar kasar mai karfin gaske ta afku ne da tsakar dare.

Gidan talabijin na kasar CCTV, ya rawaito cewa, a birnin Haidong na lardin Qinghai mai makwabtaka da inda lamarin yafi kamari mutane 11 ne suka mutu tare da jikkata 100.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayyana cewa, girgizar kasar mai karfin maki 5.9 ta yi barna sosai.

Girgizar kasa, Mutane

Abubuwan da girgizar kasar ta yi sun hada da rugujewar gidaje, tare da warwatsa mutane zuwa kan titi domin neman tsira.

An fara aikin ceto da sanyin safiyar Talata, inda shugaban kasar Xi Jinping ya yi kira da akara azama a aikin.

Ya kuma bukaci cewa a tabbatar da tsaron wadanda suka tsira da kuma dukiyoyinsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here