Nan ba da jimawa ba za mu gurfanar da VeryDarkMan a gaban kotu – EFCC

VeryDarkMan

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta ce ta kama fitattcen dan gwagwarmayar nan Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da Verydarkman kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Mai Magana da yawun hukumar Dele Oyewale ne ya tabbatar da sashen BBC Pidgin cewar sun kama verydark man din ne bayan samun jerin ƙorafe-ƙorafe akansa.

“Mun kama shi ne saboda ƙorafe-ƙorafe da takardun koke da aka kawo mana daga mutane daban-daban”, in ji Oyewale.

Sai dai da aka tambaye shi ko cikin waɗanda suka shigar mata da koke akansa akwai Bankin Guarantee Trust (GT) a ciki, Mista Oyewale ya ce “mutane daban-daban ne suka kawo musu koke, kuma hakki ne a kansu na kare masu koken.”

Karin karatu: Tawagar ƙwararru ta NAHCON ta tashi zuwa Makkah domin kaddamar da aikin Hajji

Sai dai ya ce nan gaba za su sake shi idan ya cika ƙa’idojin beli, kuma za su mika batun gaban kotu.

Hakan na zuwa ne bayan wata zanga-zanga da matasa suka gudanar kan neman a sake shi a Abuja, inda suka ci alwashin kai kokensu gaban hukumar kare haƙƙin ɗan’adam ta Najeriya kan batun.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here