Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Adamu ya ce zai zama abin kunya Shugaba Muhammadu Buhari ya mika mulki ga jam’iyyar hamayya a 2023.
Ya bayyana hakan a hirar da ya yi da BBC Hausa, shugaban jam’iyyar na kasa ya ce Buhari ya fi kowa son jam’iyyar APC ta ci zabe.
Da ya ke watsi da zargin da ake yi na cewa Shugaba Buhari na janyewa daga yi wa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, kamfen, Adamu ya ce ba daidai bane ya bar aikinsa a matsayin shugaban kasa saboda zabe.
“Abubuwa na tafiya yadda muke so, muna gode wa Allah, kowa cikin tafiyar mu na ganin Allah na tare da mu. Munyi imani da nasara, dukkan sauran jam’iyyun sun san muna gaba da su.”
Kan zargin cewa Buhari ya janye daga yi wa jam’iyyarsa kamfen, Adamu ya ce ba gaskiya bane.
“Duk wanda ya fada maka cewa ya fi Buhari son ganin jam’iyyar APC ta yi nasara karya ya ke. Dalili na shine abin kunya ne ga Shugaban kasa ya mika mulki ga jam’iyyar siyasar da ba nashi bane.”
“Abin da mutane ba su lura cewa Muhammadu Buhari shugaban kasa ne kuma akwai rantsuwa da ya yi cewa kowane dan Najeriya nasa ne. Don haka dole ya yi taka tsantsan idan ba haka ba yan adawa za su ce APC ya ke yi wa aiki a maimakon Najeriya.”









































