Dan wasan gaban Masar Mohamed Salah zai yi jinyar da za ta hana shi buga wasanni biyu na gaba a gasar Afcon 2023, sakamakon raunin da ya ji a cinyarsa.
Wasan Masar na gaba dai da Cape Verde ne a ranar Litinin.
Dan wasan gaban Liverpool ɗin mai shekara 31 kuma ba zai buga wa masar wasan zagaye na 16 ba, idan Masar ta samu nasarar tsallakawa.
Karanta wannan: Kungiyar Burnley ta dauki Fofana aro daga Chelsea
Salah ya fitra daga filin wasa yana ɗingishi a wasan da suka tashi 2-2 da Ghana tun kafin hutun rabin lokacin.
Da wannan sakamakon yanzu dole sai Masar ta doke Cape Verde da tuni ta tsallaka zagaye na gaba, domin samun damar tsallakawa zagayen ‘yan 16 a gasar.













































