Wata gobara da ta tashi a makarantar yara a China

GOBARA CHINA
GOBARA CHINA

Akalla mutum 13 ne suka mutu yayin wata gobara da ta tashi a dakin kwanan dalibai na wata makarantar da ke lardin Henan.

Ana yi wa mutum guda aiki a asibiti, wanda a yanzu jikinsa ya tsananta.

Kamfanin dillancin labaran China Xinuhua ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da daddare a wata makarantar ƙananan yara da ke yankin ƙauyen Henan.

Karanta wannan: Ganduje ya Jagoranci shugabannin APC na Kano zuwa ganawa da Tinubu a Villa

A cewar wata jaridar China wasu mutane ne ke tafiyar da makarantar da ta hada ɓangaren firaimari da na gabanin firaimari.

Tuni aka kama mai kula da makarantar aka tsare shi, yanzu kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Ba dai a bayyana su wanene suka mutu ba a hukumance, sannan ba a bayyana musabbabin faruwar gobarar ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here