Matasa a jihar Ogun, karkashin inuwar kungiyar kishin kasa ta Yewa North, sun yi tir da illolin da ayyukan kamfanin simintin Dangote ke yi a garin Ibese da ke karamar hukumar Yewa ta Arewa.
Matasan sun ce kamfanin babu wani ci gaba da taba samar wa ga al’ummarsu face gurbata musu muhalli.
Karanta wannan: Gwamnatin Kogi ta haramta bada lasisi ga masu hako Ma’adanai a Jihar
Sun bayyana kokensu ne a wata budaddiyar wasika da suka aike wa gwamnan jihar, Dapo Abiodun, ranar Juma’a.
Matasan sun kara jaddada cewa ci gaba da lalata turakun wutar lantarki a yankunan ya jefa kauyuka da dama cikin duhu.
Wasikar mai dauke da sa hannun shugaba da sakataren kungiyar, Adeyemi Sunday da Fatolu Ganiyu, ta kuma lissafo kauyukan da lamarin ya shafa da suka hadar da Joga da Iboro da Igbogila da Eegua da Igan Alade sai Ijoun da Imasayi da sauransu.
Kungiyar ta kuma koka kan yadda Dangote ya yi watsi da yarjejeniyar da aka kulla da al’ummomin yankin kafin kafa kamfanin.













































