Jirgin saman ya kama da wuta a kusa da tashar filin tashi da saukar jiragen sama ta Murtala Muhammad, inda jirgin yake kan hanyar zuwa, cewar rahoton Daily Trust.
Duk da dai cewa an ceto mutum biyu waɗanda ake tunanin su ne direbobin jirgin, ba a tabbatar da ko fasinjoji nawa ba ne a cikin jirgin saman mai saukar ungulu.
Jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) suna a wurin da hatsarin ya auku.
Ku dakaci ƙarin bayani…..