Ma’aikatar Muhalli ta tarayya, ta hannu Cibiyar gargadin Ambaliyar Ruwa a matakin farko (FEW), ta fitar da gargadi na yiwuwar ambaliya a wurare 32 da ke cikin jihohi 11 daga ranar 14 zuwa 18 ga Satumba.
A cikin sanarwar da Daraktan kula da guguwa, ambaliya da bakin teku, Usman Bokani, ya fitar a ranar Lahadi, cibiyar ta ce karuwar ruwan kogin Gongola, Benue da Niger na kara barazana ga al’umma.
Jihohin da abin ya shafa sun hada da Adamawa (Ganye da Natubi), Benue (Abinsi, Agyo, Gogo, Ito, Makurdi, Udoma da Ukpiam), Nasarawa (Agima, Rukubi da Odogbo), Taraba (Beli, Serti da Donga), Delta (Umugboma, Umukwata, Abraka, Aboh da Okpo-Krika) da kuma Rijau a jihar Neja.
Sauran wuraren sun hada da Ribah a Kebbi, Gwarzo da Karaye a Kano, Jibia a Katsina, Makira a Sokoto, sannan a Zamfara akwai Kaura Namoda, Shinkafi, Maradun, Gusau, Anka da Bungudu.
Karin labari:NiMet ta yi hasashen Ruwan sama da iska a fadin ƙasar na tsawon kwana Uku
Ma’aikatar ta yi kira ga mazauna kusa da bakin koguna, musamman daga Gongola zuwa Numan, da kuma daga Benue da Niger zuwa Lokoja, da su gaggauta barin wuraren saboda hatsarin ambaliya.
Wannan gargadin ya zo ne bayan ruwan sama mai yawa da ya sauka a Zariya, jihar Kaduna, wanda ya raba kananan yara 470 da matsugunansu tare da lalata gidaje 270 a kwanakin baya.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Kasa (NEMA) a ranar 4 ga Satumba ta bayyana cewa ambaliya ta kashe mutane 231 a bana, ta jikkata 607 yayin da mutane 114 har yanzu ba a same su ba.
A shekarar 2024 kuwa, fiye da mutane miliyan 5.2 ne suka fuskanci ambaliya a jihohi 35, inda sama da miliyan 1.2 aka raba su da gidajensu, mutane 1,237 suka mutu, yayin da 16,469 suka jikkata.












































