A wani bangare na kudurinta wajen karfafa hadin gwiwa da inganta yadda kafafen yada labarai ke ba da labarin ayyukan cigaba a cikin yanayin da dace da mutunci, Kungiyar Mata Manoma (WOFAN) ta baiwa gidajen jaridun yanar gizo biyu, wato SolaceBase da GTR Hausa motoci biyu.

Da take jawabi yayin mika motocin a Kano a ranar Laraba, Shugabar Gamayyar WOFAN, Dr Salamatu Garba, ta bayyana ‘yan jarida a matsayin muhimman abokan hulda wajen samar da cigaban ga al’umma wadanda ke gudanar da ayyukansu na yau da kullum cikin yanayi mai tsauri da wahala, lamarin da mutane kan kasa yaba gudummawarsu yadda ya kamata.
Ta kara da cewa kafafen yada labarai suna taka muhimmiyar rawa wajen sanar da jama’a da muhimman sakonnin, tabbatar da yin daidai da kara haskaka tasirin shirye-shiryen cigaba. A cewarta, wannan kyauta na nufin saukaka matsalolin sufuri da ‘yan jarida ke fuskanta da kuma inganta yadda suke gudanar da ayyukansu.

“Muna alfahari da aikin da ‘yan jarida ke yi, abokanmu ne kuma abokan hulda da al’umma ke dogaro da su yayin da suke taimakon ayyukan mu da tasirin da muke yi a tsakanin al’ummomi . Mun fahimci matsalolin sufuri da ‘yan jarida da yawa ke fuskanta, kuma wannan shi ne hanyar da muka ga za mu iya tallafa musu. Muna addu’ar Allah ya ci gaba da shiryar da su, kare su da kuma taimaka musu a hidimar da suke wa al’umma,” in ji ta.
Dr Garba ta kuma bayyana gudummawar WOFAN wajen inganta rayuwar mutane a fadin Najeriya ta hanyar karfafa mata da matasa, cigaban noma, hada da harkokin kudi, shirye-shiryen koyon sana’a, da ayyukan da ke nufin rage talauci da samar da dama mai dorewa na tattalin arziki ga al’ummomin karkara.

Da yake karbi motar a madadin SolaceBase, Shugaba kuma Mai Wallafa jaridar, Alhaji Abdullateef Abubakar Jos, ya bayyana godiyarsa ga WOFAN kan goyon baya da hadin gwiwa da take basu a tsawon shekaru.
“Mun san irin tasiri mai kyau da ayyukan WOFAN, tasharmu ta amfana da goyon bayan WOFAN ta fuskoki da dama, kamar horar da ma’aikata ciki da wajen Najeriya, kuma muna matukar godiya ga wannan kyauta mai daraja. Wannan motar za ta inganta ayyukan mu sosai kuma ta kara mana kwarin gwiwa mu ci gaba da hidimta wa jama’a. Allah Madaukaki ya saka wa Hajiya Salamatu Garba da alheri,” in ji shi.
Shima a bangarensa, Mai Wallafa GTR Hausa, Bashir Ahmad Rigasau, ya gode wa WOFAN bisa goyon bayanta ga ‘yan jarida.
“Muna matukar godiya kan goyon bayan WOFAN da kudurin ta mara adadi wajen ci gaban mu. Wannan kyauta za ta kara karfafawa da inganta ayyukanmu,” in ji shi.
SolaceBase ta ruwaito cewa a wani taron da ban, WOFAN ta baiwa wasu ‘yan jarida 3 da ke cikin tawagar kafafen yada labaraita motoci domin tabbatar hadin gwiwar da gudummawar da suka bayar wajen yada ayyukan da isar da sakon shirye-shiryen cigaba na kungiyar.













































