Kwankwasiyya ta yabawa tsofaffin masu rike da mukaman siyasa da zababbun jami’ai da suka yi murabus daga mukamansu a jihar Kano domin nuna goyon baya ga jagoranta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tana bayyana matakin a matsayin abin koyi na jarumta, biyayya da tsayawa kan ka’ida.
Wannan yabo na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Kwankwasiyya Dakta Habibu Sale Mohammed, ya fitar, inda ya bayyana cewa murabus din ya nuna gaskiya, tsayuwar ra’ayi da sadaukar da kai a wani muhimmin lokaci a tarihin siyasar jihar Kano.
A cikin sanarwar, Kwankwasiyyar ta nuna godiya ga tsofaffin kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, mataimaka na musamman, daraktocin gudanarwa da sakatarorin zartarwa da suka sauka daga mukamansu da kansu duk da rawar da suka taka wajen tafiyar da mulki da ayyukan gwamnati.
Ta bayyana cewa matakin da suka dauka, duk da sanin irin fa’idodi da damar da suka rasa, ya nuna fifita mutunci da daraja fiye da jin dadin kai.
Kwankwasiyya ta bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya taba rokon wadanda suka yi murabus da su sake duba matsayinsu, bisa la’akari da gudunmawar da suka bayar wajen gina hukumomi da inganta ayyukan gwamnati.
Sanarwar ta kara da cewa tsohon gwamnan ya dogara da ra’ayin cewa mulki ya kamata ya kasance bisa hidima ga al’umma, ba tare da daukar fansa ko tsoratarwar siyasa ba.
Sai dai Kwankwasiyyar ta ce mutanen da abin ya shafa sun tsaya kan ra’ayinsu ne sakamakon sabanin akida tsakaninsu da yadda gwamnatin jihar Kano karkashin tafiyar Gandujiyya ke gudana a halin yanzu.
Ta kuma yaba wa mataimakin gwamnan jihar da sauran zababbun jami’ai, ciki har da sanata mai ci, ’yan majalisar wakilai, ’yan majalisar dokokin jihar Kano da kansiloli, bisa ci gaba da tsayawa kan amincewar jama’a duk da matsin lamba da tayin da ake yi musu daga matakai daban-daban.
Kwankwasiyya ta jaddada cewa karfinta ya ta’allaka ne kan sadaukarwa da hidima, ba kan mukamai ko gata ba, tana mai tabbatar da cewa za ta ci gaba da kasancewa a dunkule kuma mai mayar da hankali kan muradun mabiyanta.













































