Jigawa:Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar mutum 50

flood in yobe
flood in yobe

Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 50 tare da raba mutane da dama da matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu sassan jihar.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Alhaji Yusuf Sani Babura, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Asabar a Dutse.

Sani Yusuf, ya ce ambaliyar ruwan ta lalata dubban gidaje a jihar, tare da dukiyoyin al’umma.

Ya Kara da cewa lamarin ya kuma tilastawa mazauna yankunan da Abin ya shafa fakewa a wasu wurare da suka hada da gine-ginen da gwamnati ta yi.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki mutanen da suka rasa matsugunansu idan ta Kai su sansanonin wucin gadi guda 11.

Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa mazauna kauyen Balangu ne inda akalla gidaje 237 suka ruguje tare da mutuwar mutane hudu.

A kokarin gwamnatin tarayya na tabbatar da bada agaji, ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar Farouq, ta ziyarci jihar domin raba kayan agaji.

Ta kasance a jihar ne tare da Babban Daraktan Hukumar da da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Habib, domin bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.

Ministar ta ce zuwanta jihar ya samo asali ne daga umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na bayar da tallafin da ya kamata ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.


A nasa jawabin, gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa abin da ya bayyana da daukar matakin gaggawa kan lamarin.

Sai dai Gwamna Badaru, ya koka bisa yadda ambaliyar ta afku, inda ya ce lamarin ya haifar da rudani ga wadanda abin ya shafa.

Gwamnan ya yi fatan cewa tallafin da gwamnati za ta yi zai ragewa jama’ar radadi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here