Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya IPMAN a ranar Talata ta zargi masu gidajen man fetur masu zaman kansu da janyo tashin gwauron zabin farashin mai (PMS) a wasu sassan Najeriya.
Shugaban IPMAN na kasa, Mista Chinedu Okoronkwo, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) cewa wasu daga cikin masu gidajen man ba su rage farashin ba.
NAN ta rahoto cewa har yanzu wasu ‘yan kasuwa masu zaman kansu na ci gaba da siyar da man daga Naira 180 zuwa N200 ga kowace lita a tashoshinsu, musamman a cikin yankunan jihohin Legas da Ogun.
“Wasu daga cikin mambobinmu har yanzu suna siyan kayayyaki a kan tsohon farashi, don haka ka ga wasu suna sayar da fiye da farashin da aka amince da su na N165.
“IPMAN tana kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su jawo wadannan masu gidajen man domin su koma ga tsohon tsarin farashi domin a samu daidaito a farashin man fetur,” inji shi.
Okoronkwo ya ce karancin mai da aka fuskanta a fadin kasar nan a makonnin da suka gabata ya kusa kawo karshe.
Ya shawarci kamfanin man fetur na kasa (NNPC) Ltd., da ya kara yawan man da ake kaiwa Fatakwal, Calabar da sauran yankunan bakin ruwa domin tabbatar da an raba su cikin sauki.
Dangane da biyan diyya ga masu ababen hawa da man fetur din da aka shigo da su daga waje ya shafa, ya ce ‘yan kungiyar IPMAN na ci gaba da tattara jerin sunayen wadanda za a duba su.













































