Jam’iyyar ADC ta kori dan takarar ta na shugaban kasa Mista Dumebi Kachikwu daga jam’iyyar baki daya.
Cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na kasa Ralphs Nwosu ya fitar a karshen mako, ta ce an kori Kachikwu ne dalilin yakar jam’iyyar da kuma saba kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Ta ce wani kwamitin mutum bakwai da jam’iyyar ta kafa wanda ya shafe kwanaki shida ya mika rahoton sa a ranar Alhamis gameda zarge zargen da ake musu.
Sanarwar ta ce a ranar Juma’a ne kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya tattauna kan rahoton tare da karbar rahoton kwamitin dan yimasa gyara.
Sauran mambobin da aka kora daga jam’iyyar sun hada da Kennedy Odion da Kingsley Oggah se Musa Hassan da Bello Isiyaka da Clement Ehiator se Kabiru Hussaini da Alaka Godwin.
Ya kara da cewa: “Kwamitin ladabtarwa me mutum bakwai da jam’iyyar ADC ta kafa domin duba zarge-zargen da ake yi na rashin da’a da sauran su da ake zargin Mista Kachikwu da sauransu ya zauna a ranakun 8, 9, 10, 12, 13 da 14 ga watan Satumba, sannan ya mika rahoton sa a hukumance ga shugabannin jam’iyyar a ranar 15 ga Satumba 2022.










































