Sanata Adamu Aleiro wanda shine tsohon gwamnan jahar Kebbi, kuma sanata ne mai ci a majalisar dattawan Najeriya, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar a yau Alhamis.
Ya kuma baiyana fitar tasa ne a Birnin Kebbi, inda yace ya yinke hukuncin fitar tasa ne daga jam’iyyar ta APC domin ya cikawa magoya bayansa burin su.
Ya kara da cewa kafin ya yanke hukun cin fitar tasa, ya yi kokari wajan yaga an sasan ta dashi akan matsalolin sa da jam’iyyar, amma uwar jam’iyyar ta kasa bata yi komai akai ba.
A karshi ya nemi magoya bayan sa a fadin jihar ta Kebbi dasu zabe jam’iyyar PDP a kakar zaben bana
(NAN)













































