‘Yan uwan wadanda aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun karyata sakin fasinjojin

Abuja Kaduna train
Abuja Kaduna train
‘yan-uwan wadanda aka sace a jirgin kasar da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sun karyata labarin da ake yadawa a shafikan sada zumunta cewa an saki ‘yan uwan na su.
Hakan na dauke cikin wata sanarwa da shugabanin kungiyar ‘yan-uwan wadanda aka sace Dr AbdulFatai Jimoh da Dr Ba’aba Muhammad suka fitar, inda suka ce labarin kazan kurege ne kawai.
Hakan dai ya biyo bayan wani labara da ke yawo a shafikan sada zumunta cewa an saki wata tsohowa ‘yar shekara 85 tare da ‘yar ta, harma suna karbar kulawar likitotci a asibiti.

Har yanzu dai babu wani labari game da cigaba da aikin jirgin kasan Abuja-Kaduna tun bayan yunkurin cigaba da aikin da ya yi karo da zanga-zangar ‘yan-uwan wadanda aka sace a Kaduna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here