Sarkin da yafi kowan-ne da-dewa a jihar Zamafara ya rasu

Alhaji Ahmad Umar Mai Kwatarshi 750x430 1
Alhaji Ahmad Umar Mai Kwatarshi 750x430 1

Sarkin Kwatarkwashin Jihar Zamfara, Alhaji Ahamad Umar ya rasu a jiya Alhamis yana mai shekara 93.

Sarkin shine wanda yafi kowanne da dewa a karagar milki, wanda ya kai shekara 61 yana mulkin Kwatarkwashi da ke karamar hukumar Bungudu a cikin jihar Zamfara.

Sakataran gwamnatin Jihar ta Zamfara, Alhaji Kabiru Balarabe ne ya sanar da rasuwar tasa a wata sanarwa da ya fitar, ya ce sarkin ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Ya kara da cewa anyi jana’izar sa da misalin karfe 6:30 pm a garin na Kwatarkwashi da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya rawaitu cewa, an nada sarkin Kwatarkwashin a shekarar 1961, wanda Sultan Abubakar na uku ne ya nada shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here