Tsohon minista mai kula da al-amuran yakin Niger Delt, sanata Godswill Akpabio ya zama dan takarar sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta arewa maso gabas a karkashin tutar jam’iyyar APC.
Baturan zaben da ya kula da zaben fitar-da-gwani da aka gudanar ranar Alhamis, a karamar hukumar Ikot Ekpene da ke jihar Akwa Ibom, Ibom Bunmi Moloye ya ce cikin daliget 512 da aka tantan ce, guuda 478 sun zabe Akpabio, yayin da guda 3 suka zabe DIG Ekpo Udom (Rtd.), in da kuma Joseph Akpa ya sami kuri’a daya.
Idon za’a iya tunawa dai an fitar da ‘yan takarar masalaha a ran 28 ga watan da ya wuce, daga baya kuma aka suke ‘yan takarar saboda korafe korafen da aka shigar.
Yayin jawabin sa, sanata Akpabio ya godewa mutanan Akwa Ibom yankin arewa maso gaba bisa kara bashi dama ya wakil ce so a majalisar dattawan Najeriya.













































