2023: Zama na abokin takarar Atiku, yin Allah ne-Okowa

Ifeanyi Okowa
Ifeanyi Okowa

Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Dakta Ifeanyi Okowa, ya ce zaman sa abokin takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Atiku Abubakar, yin Allah ne.

Dakta Okowa, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da kafafen yada labarai a Kano, a daren ranar Talatar da ta gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa tun bayan zaben Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar a zaben shekara mai zuwa ta 2023, aka fara samun cece-kuce daga bangaren gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, wanda ke tunanin shi za a zaba.

A cewar Okowa, duk wadanda aka yi la’akari da su a lokacin zaben sun cancanta kamar yadda shi ma ya cancanta.

“Batun wanda bai ji dadin zabar sa ba kuma a cewar sa siyasa ce kuma za a magance matsalar nan ba da jimawa ba.”

”Tsarin da nake da shi a harkokin mulki da kuma matsayina na dan siyasa mai kishin kasa wanda ya fara siyasa tun daga matakin kananan hukumomi a shekarar 1991, na daga cikin abubuwan da dan takarar shugaban kasar ya yi la’akhari da su.

“Na yi imanin zabi na a matsayin abokin takara shi ne mafi dacewa ga jam’iyyar PDP idan batun lashe zaben shekarar 2023, ake yi” in ji Okowa.
”Ba wai ina fadar haka bane domin ni ne abokin takararsa, amma a gaskiya Atiku ne ya fi dacewa da kujerar shugaban kasa”.

“Nijeriya a halin yanzu tana bukatar dan takarar shugaban kasa mai dimbin kwarewa, domin aikin ba na ‘rago ba ne’’.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here