DA DUMI-DUMI: Gwamna Ganduje ya ki amincewa da murabus din shugaban KAROTA Baffa Babba Dan-agundi

Baffa Babba Dangundi KAROTA MD
Baffa Babba Dangundi KAROTA MD

Mukaddashin gwamnan jihar Kano, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a ranar Litinin ya yi watsi da murabus din Manajan Daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA), Baffa Babba Dan-agundi.

Rahotanni sun bayyana cewa Dan-agundi ya rubuta kuma ya mika wa mukaddashin gwamnan takardar murabus dinsa a yau, amma gwamnan da ke hutu a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ya umarci mukaddashin gwamnan da ya ki amincewa da takardar.

Da yake magana da Solacebase kan batun, Manajan Daraktan KAROTA, Baffa Babba Dan-agundi ya tabbatar da kin amincewa da murabus din da gwamnan yayi.

“Kun ga gwamna ba wai ubangidana ne kawai ba, kamar uba ne a gare ni, don haka dole ne na amince da duk abin da ya gaya mani,” Baffa ya shaidawa Solacebase.

‘’Gwamna Ganduje shi ne wanda ya ba ni wannan mukamin na Manajan Darakta wanda ya daga matsayina a siyasance.

Da Solacebase ta tambaye shi dalilin yin murabus din Baffa ya ce, a gaskiya ina so in ci gaba da burina na siyasa na tsayawa takara amma duk sai na jira matakin da gwamna zai dauka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here