Ministan tsaro ya buƙaci a rungumi tsarin tattaunawa da neman shawar don samun zaman lafiya a yankuna

WhatsApp Image 2025 09 19 at 15.59.52 1 1024x686 1 750x430

Ministan tsaro na Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya bukaci shugabannin duniya da su rungumi tattaunawa da shawartawa a matsayin muhimman matakai na gina zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.

Ya bayyana hakan ne a lokacin taron Beijing Xiangshan Forum karo na 12 da aka gudanar a kasar Sin a makon da ya gabata, inda ya gabatar da jawabi a zaman taro na huɗu mai taken “Gina Zaman Lafiya ta hanyar Tattaunawa da Shawartawa: Tsarin Zaman Lafiya Mai Ɗorewa.”

Karin labari: UNGA: Shettima zai gabatar da jawabin kasa na Najeriya a yau Laraba

A gaban shugabannin tsaro, jakadun ƙasashe, masu tsara manufofi da masana daga sama da ƙasashe 100, minista Abubakar ya jaddada cewa tattaunawa ita ce mafi inganci wajen hana rikice-rikice da kuma samar da zaman lafiya.

Ministan ya bayyana kokarin Najeriya wajen samar da zaman lafiya, inda ya kawo misalan shigar ƙasar cikin ayyukan kungiyar ECOWAS a kasashen Liberia, Saliyo da Gambiya, da kuma hadin gwiwar Multinational Joint Task Force wajen yaƙi da Boko Haram.

Haka kuma ya ambaci shirye-shiryen cikin gida irin su Shirin Afuwa ga ‘Yan Niger Delta da shirin tafiya ga tubabbu wato Operation Safe Corridor, waɗanda ya ce suna nuna amincewar Najeriya wajen warware rikice-rikice ta hanyar haɗin kai, sahihanci da tattaunawa mai fa’ida.

Abubakar ya danganta wannan saƙo da Shirin Sabon Fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce gwamnati na mai da hankali kan tsaro, zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

A cewarsa, rawar da Najeriya ke takawa a yankin na nuna ƙudurin ƙasar na bunƙasa zaman lafiya ta hanyar haɗin gwiwar ƙasashe da tattaunawa.

Ya kammala da kira ga ƙasashe su rungumi alhakin bai ɗaya wajen kiyaye tsarin duniya, yana mai cewa: “Ta hanyar ci gaba da shawarta da haɗin kai, ƙasashe za su iya gina zaman lafiya mai haɗawa, mai ɗorewa kuma mai jure wa ƙalubale.”

Jawabin nasa ya sake tabbatar da matsayi na dabarun Najeriya wajen tsara tsare-tsaren tsaro na yankuna, tare da aiwatar da manufar Sabon Fata zuwa aiki a zahiri a gida da waje.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here