Kano: Sanata Barau ya baiwa shugabannin APC motoci 61 babura 1,137

WhatsApp Image 2025 02 23 at 19.05.54 750x430

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin, a ranar Lahadi, ya raba motoci 61 da babura 1,137 ga shugabannin jam’iyyar APC na jihar.

Taron wanda ya gudana a dakin taro na Meena Event Centre dake kan titin Lugard, ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar, ciki har da shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa an raba motocin da babura ne ga shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 44 da unguwanni 484 na jihar Kano a wani mataki na karfafa musu gwiwa.

A cikin wata sanarwa da mai baiwa mataimakin shugaban majalisar dattijai shawara kan harkokin yada labarai Ismail Mudashir ya fitar a ranar Lahadi, ta rawaito cewa yayin da yake jawabi ga dimbin jama’a, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya ce mataimakin shugaban majalisar dattawan ne ke ba da kudaden gudanar da ayyukan jam’iyyar tun lokacin da jam’iyyar (NNPP) ta karbi ragamar mulkin jihar a shekarar 2023.

Ya bayyana Barau a matsayin Sanata ga kowa da kowa a jihar Kano: “Barau shine Sanata ga kowa da kowa a jihar Kano, shi ke wakiltar Kano ta Arewa, amma na mutanen Kano ta tsakiya ne, da Kano ta Kudu da kowa da kowa

Ya ce a shekarar 2027, za a tantance masu neman tsayawa takara bisa la’akari da irin gudunmawar da suka bayar wajen ciyar da jam’iyyar gaba tun daga 2023.

A nasa bangaren, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Albarkatun Man Fetur Alhassan Ado Doguwa, ya ce da hadin kan da ke tattare da jam’iyyar APC a Kano, za a kayar da jam’iyyar (NNPP) kafin karfe 1:00 na rana. a ranar zabe a 2027.

A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yabawa mataimakin shugaban majalisar dattawa bisa wannan hoɓɓasa sannan ya bukaci sauran su yi koyi da shi.

A nasa bangaren, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin, ya bayyana karfafawa yan jam’iyya a matsayin yunkurin ciyar da ita gaba.

Ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana da shirye-shirye daban-daban da aka tsara domin karfafawa ‘yan Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here