Kungiyoyin farar hula a Kano sun gargadi ’yan sanda kan cin zarafi yayin binciken Ja’afar Ja’afar

Jaafar

Ƙungiyoyin farar hula a jihar Kano sun nuna damuwa kan gayyatar da rundunar ’yan sanda ta yi wa mai jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar, inda suka bukaci a gudanar da bincike cikin gaskiya ba tare da wani nau’in danniya ta siyasa ba.

Wannan gayyata ta taso ne daga umarnin Kotun Majistire mai lamba 15 a Nomansland, Kano, sakamakon korafin da Abdullahi Ibrahim Rogo, Daraktan Fadar Gwamnan Kano, ya shigar kan batun batanci da tayar da husuma.

Sai dai kungiyoyin sun tunatar da cewa jaridar ta riga ta wallafa binciken satar Naira biliyan 6.5 daga ofishin Rogo, abin da yanzu haka hukumar EFCC da ICPC ke bincike.

Kungiyoyin sun ce kodayake ’yan sanda suna da hurumin bincike, bai kamata a yi amfani da su wajen danniya ko hana ’yan jarida yin aikinsu ba.

Sun jaddada cewa ’yan jarida su ne masu kare dimokuradiyya da kuma murya ga marasa murya a cikin al’umma.

Sun kara da cewa yunkurin tsoratarwa ko shigar da shari’o’in karya kan ’yan jarida na tauye ’yancin fadin albarkacin baki da ’yancin kafafen yada labarai da kundin tsarin mulki ya tanada, lamarin da ke raunana dimokuradiyya.

Kungiyoyin sun kuma yi Allah wadai da amfani da hukumomin gwamnati wajen rufe bakin masu sukar gwamnati, suna gargadi cewa hakan yana lalata amincewar jama’a tare da karfafa cin hanci.

Sun roki kotuna su guji bayar da umarnin da za a iya amfani da shi wajen danne murya.

A karshe, sun tabbatar da goyon bayansu ga ’yan jarida musamman masu binciken cin hanci, suna mai cewa yakin da ake yi da rashawa ya kamata a yaba wa ’yan jarida ba a tsananta musu ba.

Jimillar kungiyoyi 22 ne suka rattaba hannu kan sanarwar, ciki har da ƙungiyar ci gaban Wuro da Cibiyar Kare Haƙƙin Dan Adam da Ƙarfafa Ci gaban Jama’a da kuma ƙungiyar haɗin kai don ci gaban Dimokuradiyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here