Kano ta bayyana tsarin samar da ci gaban mai dorewa ga al’ummar karkara

Murtala Garo

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudurin ta na inganta ci gaban al’ummar karkara mai dorewa ta hanyar kara karfafa hadin gwiwa da manyan masu ruwa da tsaki.

Gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Mataimakin sa, Alhaji Murtala Sule Garo, ya wakilta, ne ya bayyana hakan a wajen taron samar da ci gaba mai dorewa ga al’ummar karkara (RUSCODS 2026) da aka gudanar a dakin taro na Coronation da ke Gidan Gwamnati Kano a ranar Talata.

Da yake jawabi game da taken taron, “Hanyar Hada Gwiwa Domin Ci Gaban Al’ummar Karkara Mai Dorewa a Jihar Kano”, ya ce cigaban Jihar Kano na da alaka ta kai tsaye da karfafa al’ummomin karkara, inda noma, ciniki da kananan sana’o’i suka kasance manyan hanyoyin samun abinci.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ofishin mataimakin gwamna, Lurwanu Idris Malikawa Garu, ya fitar, ya ce Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin yanzu ta himmatu wajen tabbatar da cewa ba a bar wata al’umma a baya ba, yana mai jaddada cewa gwamnati kadai ba za ta iya samar da ci gaba mai dorewa ba.

Alhaji Murtala Sule Garo, yayin da ya ke ambato matsalolin da yawancin al’ummomin karkara ke fuskanta, ya ce magance wadannan matsalolin na bukatar karfafa hadin kai tsakanin gwamnati, abokan hulda a fannin ci gaba, cibiyoyin kudi, kungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya da al’ummomin cikin gida.

Ya bayyana gudummawar gwamnati wajen gina titunan a karkara, ruwan sha mai tsafta, wutar lantarki, kiwon lafiya, ilimi, noma, samar wa matasa sana’a da shirye-shiryen fuskantar sauyin yanayi da nufin inganta rayuwa da damar fadada tattalin arziki a fadin jihar.

Da yake nema a hada gwiwa, Garo ya ja hankalin abokan hulda a fannin ci gaba, kamfanoni masu zaman kansu da shugabannin al’umma da su daidaita ayyukansu da bukatun al’ummomin karkara.

Ya kuma ja hankalin mahalarta taron da su kawo shawarwari masu amfani, yana mai cewa, “Za mu ci gaba da maraba da duk wani hadin gwiwa mai kyau da zai ba da gudummawa wajen jin dadin jama’a da ci gaban jihar mu.”

A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Karkara da Cigaban al’umma, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, ya bayyana cewa taron na 2026–2030 an tsara shi ne domin canza irin tsarin da ake kai.

“Yana ba da cikakken tsari na shekaru biyar wanda ya sanya al’ummomin karkara fifiko domin tsara ci gaba” in ji shi.

Haka kuma, Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Maharaz, wanda ya yi magana a madadin Sarakunan Kano, Rano da Gaya, ya ce taron ya ba da dama don yin tunani sosai kan halin da al’ummomin karkara ke ciki.

“Wannan dandali ne na hada ra’ayoyin mu da gano mafitar da za ayi aiki da ita don inganta rayuwar al’ummar karkara,” in ji Sarkin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here