Gwamnan Osun Adeleke ya nada diyar sa a matsayin kwamishina.

Ademola Adeleke and Adenike

Majalisar dokokin jihar Osun a ranar Juma’a 7 ga watan Yuli, 2023, ta tabbatar da jerin sunayen kwamishinoni 25 da aka mika wa majalisar domin tantancewa tare da tabbatar da su ga gwamna Ademola Adeleke.

Kakakin majalisar, Adewale Egbedun, wanda ya bayyana sunayen a yayin zaman majalisar ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Ya ce kwamishinoni 25 da aka nada sun hada da Oladosu Babatunde, Bayo Ogunbamgbe, Sesan Oyedele, Kolapo Alimi, Soji Adeigbe, Moshood Olagunju, George Alabi da Sunday Oroniyi.

Sauran sun hada da Abiodun Ojo da Bashir Salami da Moruf Ayofe da Sola Ogungbile da Bunmi Jenyo da Ayo Awolowo da Wole Bada da Dipo Eluwole da Rasheed Aderibigbe da Moruf Adeleke da Adeyemo Ademola da Olabiyi Odunlade da Jola Akintola da Mayowa Adejorin da Adenike Adeleke da Tola Gani Ola-Oluwa.

Adenike Adeleke tauraruwar Instagram ce wacce ke amfani da dandalin don tallata kayan kwalliya da rayuwarta ta yau da kullun.

Ita dai Adenike Adeleke an haifa ta ne a ranar 17 ga Maris, 1995.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here