Wani Lauya da kungiyar fararen hula sun maka gwamnatin Kano da wasu mutane 2 a kotu bisa zargin kin samun adalci

500EE865 9C82 4ECF 8119 B91B151766E8
500EE865 9C82 4ECF 8119 B91B151766E8

Wani lauya mai suna Yushau Sani Yankuzo da kuma kungiyar Human Rights and Social Advancement CEFSAN sun maka babban lauyan jihar Kano da kuma  gwamnatin jihar Kano a gaban kotu bisa kara musu kudaden da ake biya yayin shigar da kara wanda hakan ya sabawa kundin tsarin mulki.

A wata takardar sammace mai dauke da kwanan watan Fabrairu 10, 2022, masu shigar da kara na kalubalantar makudan kudade da hukumar shari’a ta jihar Kano ke sanyawa wajen aiwatar da shari’o’in da suka shafi hakki.

Masu shigar da kara a karar sun ce matakin da bangaren shari’a na jihar Kano karkashin jagorancin Alkalin Alkalai, Mai shari’a Nura Sagir Umar ya dauka na kara kudin ya saba wa kundin tsarin mulki domin ikon yin hakan ya rataya ne kawai ga Alkalin Alkalan Tarayya.

Sai dai a wata sanarwa da masu shigar da kara suka fitar kuma suka aika wa Solacebase a ranar Juma’a, ta ce Alkalin Alkalan Jihar Kano, Mai shari’a Nura Sagir Umar ya fitar da wata doka mai dauke da kwanan watan 22 ga watan Fabrairun 2022, inda ya yi kari ga  kudin shigar da karar daga N5,000 zuwa Naira 1,000 ga ko wace kara ko kudiring gaggawa.

Masu shigar da kara a cikin sanarwar sun bayyana matakin da hukumar shari’a ta jihar Kano ta dauka a matsayin hana ‘yan kasa samun adalci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here