Gwamnatin tarayya ta ce kawo yanzu Najeriya ta yi asarar sama da Naira biliyan 1.3 sakamakon barkewar cutar Tuta absoluta da aka fi sani da “Ebolar Tumatir” a jihohi uku.
Sanatq Abubakar Kyari, ministan noma da samar da abinci ne ya bayyana haka a taron karawa juna sani na kwana hudu da ake gudanarwa a cibiyoyin hada-hadar kudi a ranar Laraba a Abuja.
HortiNigeria ne suka shirya taron bitar tare da hadin gwiwar Nigeria Incentive-Based Risk Sharing System for Agricultural Lending (NIRSAL) Plc.
Kyari ya ce, sakamakon haka ya haifar da karuwar farashin kwandunan tumatur kilo 50 daga Naira 5,000 zuwa Naira 10,000 da kuma kusan Naira 30,000 wanda hakan ya ta’azzara hauhawar farashin kayayyaki da kuma tabarbarewar kasafin kudi.
Labari mai alaƙa: Manoman tumatur sun yi hasashen fuskantar karancin Tumatir saboda barkewar annobar cutar Tuta Absoluta
A cewarsa jihohin da aka samu asarar sun hada da Kano, Katsina da kuma Kaduna.
Ya bayyana cewa cutar ebola ta tumatur ta kara nuna gazawar tsarin noman a kasar nan inda ya kara da cewa ƙwarin da ke damun tumatur na iya lalata amfanin gonar tumatir a cikin sa’o’i 48, wanda hakan zai haifar da mummunar asarar amfanin gona.
A cewarsa, wannan matsalar ta nuna bukatar gaggawar samar da dabarun yaki da kwari, da zuba jari a irin nau’in amfanin gona mai jure wa da kuma habaka tallafi ga manoma domin kare harkar samar da abinci a kasar.(NAN) (www.nannews.ng