Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu a karkashin inuwar jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Sanata Kawu Sumaila, ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabi, ya karanta wasikar ficewar dan majalisar a zauren majalisar a ranar Laraba.
A cewar Sumaila a cikin wasikar tasa, ya ce yanke shawarar barin jam’iyyar ta NNPP ya ta’allaka ne a kan abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar da ba za a iya musantawa ba, wadanda suka janyo rarrabuwar kawuna da kuma tabarbarewar harkokin jam’iyyar.
Wasikar dai mai suna “Sanarwar sauya sheka daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC).
Karin karatu: Najeriya ta yi asarar Naira Biliyan 1.3 sakamakon cutar Ebolar Tumatir a jihohin Kano, Katsina, Kaduna – Minista
“A bisa sashe na 68, karamin sashe na 1 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima, na rubutawa shugaban majalisar dattawa a madadin majalisar dattawa.
Dan majalisar ya kara da cewa, wani abin da ke kara bayyana wannan rarrabuwar kawuna shi ne kasancewar bangarori da dama kowanne da tambarin jam’iyyarsa.
Wannan, ya yi nuni da zurfin rarrabuwar kawuna a bainar jama’a na jam’iyyar ta fuska da ma’ana, domin an raba jam’iyyar a tsari da ma’ana.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, bayan ficewar Sumaila zuwa APC daga jam’iyyar NNPP, yawan sanatoci a dandalin NNPP ya ragu zuwa biyu.
NAN ta kuma ruwaito cewa, Sanatoci a jam’iyyar APC a yanzu sun karu zuwa 65, yayin da PDP ke da 33, Labour Party, biyar, SDP, biyu da APGA daya, wanda ya kawo adadin Sanatoci 107, da kujeru biyu.
Kujeru biyu da ba kowa ba, su ne na Anambra ta Kudu da rasuwar Sanata Ifeanyi Ubah a 2024 da Edo Central, bayan zaben Sanata Monday Okpebholo a matsayin Gwamnan Edo. (NAN)