Keyamo ya bayyana Dalilan da suka kawo jinkirin fara yakin neman zaben Shugaban kasa na APC

Festus Keyamo new
Festus Keyamo new

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ce an jinkirta kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na shekarar 2023 domin tabbatar da kammala kowanne irin shiri dan tunkarar sa.

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa Mista Festus Keyamo ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja bayan kammala taron Kwamitin koli da kungiyar gwamnoni.

“Yakin neman zaben mu abune tamkar munata dora kaya a tirela ne mai nauyin ton 50, ka ga da zarar mun dau hanya se dai wani labarin.

“Don haka abin da muke yi ke nan, shugaban kasa ne shugaban kwamitin yakin neman zaben, kuma za mu yi la’akari da dukkan da ya bamu.

Keyamo ya ce, Tinubu zai gabatarwa da ‘yan Najeriya kundin manufofin sa nan ba da dadewa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here