
Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta ce ta fara wani gagarumin shiri na daukar matakai domin dakile hare-haren ‘yan bindiga.
Hakan ya biyo bayan sace wasu ‘yan mata shida da aka yi a karamar hukumar Bwari da ke birnin tarayya a makon jiya.
Karanta wannan: ‘Yan sanda sun yi fatali da sace matafiya a hanyar Abuja zuwa Kaduna
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Muyiwa Adejobi ya fitar a ranar Lahadi ta ce, “Hedikwatar ‘yan sandan na ci gaba da hada kai don ganin an shawo kan lamarin tare da hana sake afkuwar lamarin.
Karanta wannan: NITDA zata samar da cibiyar kere-kere ta zamani a Kano
Idan dai za a iya tunawa, tun daga watan Disambar 2023, babu wani mako da ya wuce ba tare da rahoton hare-haren ‘yan bindiga da sace-sacen mutane ba, musamman a yankunan da ke makwabtaka da jihohin Kaduna da Neja da Nasarawa da kuma Kogi.
Al’ummomin da ke nesa kamar Kuduru da Gbaupe da Katari da Kawu da Arab Road a Kabwa da Dei-Dei da kuma wasu a Kuje sun fi shiga tashin hankali.