Da yammacin Talatar nan ne ƴan bindiga suka yi awon gaba da fasinjoji da dama a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a wani samame da suka kwashe kusan sa’a guda suna yi.
Rahotonni sun bayyana cewa, ƴan bindigar sun tare babbar hanyar da ke tsakanin Kurmin Kare zuwa Katari a ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da fasinjoji daga cikin motocin haya har ma da na gida.
Wani ganau ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a Katari da misalin karfe 4:30 na yamma.
Haka kuma ya bayyana cewa, akwai motoci da dama da babu kowa a gefen titi, wanda ke nuni da cewa an yi garkuwa da mutanen da ke cikinsu ne ko kuma sun gudu cikin daji.
Ya ce bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro da dama sun isa wurin domin shawo kan matsalar.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an tsaro sun yi musayar wuta da ƴan bindigar amma ba a kai ga gano adadinsu ba.













































